Macron wanda ya dade yake kare matsayin da kasar ta dauka na gudanar da bikin bude wasanni a bakin teku, sabanin yadda aka saba yi a filin wasanni, ya jinjinawa jami'an tsaro da kuma wadanda suka taka rawa wajen samun nasarar bikin bude gasar.
Tsaunin Eiffel Tower AP - David J. PhillipMacron yace shekaru 7 da suka gabata, kowa ya shaida musu cewar ba zai yiwu ba a gudanar da irin wannan biki a bakin teku, amma kuma yau duniya ta gani.
Shugaban yace masana daban daban sun bayyana fargaba game da barazanar tsaro, yayin da wasu suka ce 'yan ta'adda na iya yiwa bikin illa, amma yau ga shi kowa ya ga nasara da aka samu.
Macron yace anyi amfani da 'yan sanda da jandarmeri dubu 45 wajen sanya ido lokacin bikin bude gasar, yayin da ake saran jami'an tsaro dubu 250 su yi aiki lokacin wasanni baki daya.
Bikin bude wasannin Olympics AP - Richard HeathcoteShugaban yace duk da nasarar da aka samu wajen bude bikin fara wasannin, har yanzu da sauran rina a kaba, dangane da tabbatar da tsaron 'yan wasa da bakin da suka halarci gasar a makwanni masu zuwa da kuma gasar Olympics ta masu fama da nakasa da ake kira Paralympics da zai biyo baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI