Falasɗinawa sun ce basa tunanin samun sauyi daga zaɓen Amurka

Falasɗinawa sun ce basa tunanin samun sauyi daga zaɓen Amurka

Falasɗinawan mazauna Ramallah sun ce babu wani banbanci tsakanin Harris wadda yanzu haka ita ce mataimakiyar shugaba Biden da kuma Trump wanda a lokacinsa aka mayar da birnin Ƙudus babban birnin kasar Isra'ila.

Falasdinawa sama da dubu 43 Isra'ila ta kashe a yakin da ta kaddamar tun watan Oktobar bara a garuruwansu, kuma cikin su har da tarin mata da ƙananan yara, baya ga wasu mutane sama da dubu 100 da suka jikkata.

Mahmoud Nawajaa, jami'in da ke jagorancin ƙauracewa sayen kayan da Isra'ila ke sarrafawa a Ramallah, ya ce basa tunanin wani abu na iya sauyawa a yankin na su koda wanene ya samu nasarar zaben da ake gudanarwa yau a Amurkan.

Nawajaa ya ce kisan kiyashin da ake yi wa jama'arsu a yankin Gaza tare da wasu laifuffukan da ake aikatawa a Falasɗinu da kuma Lebanon ba masu yiwuwa ba ne idan babu goyan bayan Amurka.

Jamal Juma, jami'in kungiyar yaƙi da wariyar jinsin da ake nunawa Falasɗinawa ya ce su da Ubangiji suka dogara amma ba daga sabon shugaban ƙasar da za'a zaɓa ba.

Juma ya gabatar da misali da yadda a shekarar 2017 Trump ya goyi bayan mayar da cibiyar Isra'ila Birnin Kudus, yayinda shi kuma shugaba Biden ya ci gaba da goyan bayan kisan gillar da ake yiwa Falasdinawa.

Osama Abdel Karim, ya ce basa tunanin samun wani abu daga sabuwar gwamnatin Amurka mai zuwa, saboda matsayin kasar na ci gaba da goyan bayan Israila da muradunta a ko da yaushe.

Abdel Karim ya ce a bayyane ya ke cewar Amurka ce ke ɗaukar nauyin yaƙin da Isra'ila ke yi wajen bata kudade da kuma makaman da ake kashe jama'arsu da shi, duk da matsayin ta na iƙirarin goyan bayan dimokiradiya da kuma kare hakkin Bil Adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)