Falasɗinawa 90 sun isa gida ƙarƙashin yarjejeniyar Hamas da Isra'ila

Falasɗinawa 90 sun isa gida ƙarƙashin yarjejeniyar Hamas da Isra'ila

Bayanai sun ce galibin wanda Isra’ilar ta saki mutane ne da ta kame a baya-bayan nan sakamakon wallafe-wallafe da suka yi a shafukansu na sada zumunta saboda kisan ƙare dangin da ƙasar ke musu na tsawon watanni, kuma dukkaninsu mata ne.

Wasu daga cikin matan da suka koma gida ƙarƙashin yarjejeniyar Isra'ila da Hamas. Wasu daga cikin matan da suka koma gida ƙarƙashin yarjejeniyar Isra'ila da Hamas. © Mussa Issa Qamasma / Reuters An yi ta murna tare da harba tartsatsin wuta bayan isowar motar da ke ɗauke da fursunonin na Falasɗinu bisa jagorancin ƙungiyar Red Cresent. Wasu motoci maƙare da kayan agaji da suka shiga yankin Gaza na Falasɗinu. Wasu motoci maƙare da kayan agaji da suka shiga yankin Gaza na Falasɗinu. REUTERS - Mohamed Abd El Ghany A gefe guda manyan motocin dakon kaya aƙalla 900 ne ke ci gaba da shiga Gaza maƙare da abinci da ruwan da sauran kayankin buƙata a wani yanayi da Falasɗinawa ke ci gaba da laluben gidajensu da Isra’ila ta rushe su baki ɗaya.

Wasu Falasdinawa da ke ƙoƙarin komawa gidajensu bayan fara aikin yarjejeniyar. Wasu Falasdinawa da ke ƙoƙarin komawa gidajensu bayan fara aikin yarjejeniyar. © AP/Fernando Vergara An ga yadda ayarin Falasɗinawa wasu a ƙafa ko kuma a ababen hawa ke ci gaba da tururuwa don komawa yankin arewacin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)