Wata daga cikin wadanda suka samu mafaka a tsohon gidan yarin, Yasmeen al-Dardasi ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewar suna ji suna gani suka wuce wasu mutanen da suka samu raunuka daga hare haren Isra'ila domin barin Khan Younes domin zuwa gidan yarin don tsira da rayukansu.
al-Dardasi tace sanda suka kwana a karkashin wata bishiya kafin isa ga gidan yarin da yanzu haka ya zama mafakarsu.
Ta kara da cewa, mijinta na fama da ciwon koda, kuma huhunsa guda kawai yake aiki, ga shi inda suke ko katifa babu.
Falasdinawan da suka rasa matsugunansu sun ce babu wani wuri da ya rage Isra'ila bata kai hari ba, daga makarantu zuwa asibitoci da kuma sansanin 'yan gudun hijira.
Ko a makon nan sanda Isra'ilar ta kai harin da ya hallaka mutane sama da 90 a sansanin 'yan gudun hijira.
Ko a yau Isra'ila ta kai harin da ya kashe mutane 30 a wata makaranatr dake Deir Al-Balah, tare da kai wasu hare haren asibitin da aka kai wadanda suka samu raunuka.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ce cewa ana ci gaba da tattauna shirin tsagaita wutar da shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI