Falasdinawa sun fara neman 'yan uwansu da suka makale a karkashin gine gine

Falasdinawa sun fara neman 'yan uwansu da suka makale a karkashin gine gine

Mahmoud Basal, mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa ta Falasdinawa yace suna neman akalla mutane 10,000 da suka yi shahada a karkashin gine ginen saboda bama baman da aka yi amfani da su wajen rusa gidajen su.

Jami'in yace akalla gawarwaki 2,840 sun narke kuma babu alamunsu a yankin.

Majalisar dinkin duniya ta ce akalla sama da kashi 90 na gidajen dake Gaza sun ruguje sakamakon hare haren da Isra'ila tayi ta kai wa a yankin, yayin da wani jami'inta ke cewa sharar dake yankin daga gidajen da suka rushe ta kai tan 50, kuma ana iya kwashe shekaru 21 kafin kwashe ta baki daya, yayin da kudin kwashe ta ka iya kai wa dala biliyan guda da miliyan 200.

Wani rahotan majalisar ya ce ana iya kai wa shekarar 2040 kafin sake gina Gazar, yayin da wani jami'in ci gaba na majalisar ya ce yakin ya mayar da ci gaban Gaza shekaru 69 baya.

Isra'ila ta ce burin ta na yakin shine murkushe daukacin Hamas da kuma lalata hanyoyin da take da shi a karkashin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)