Falasdinawa na zaman dar-dar ganin yadda Isra’ila ke barazanar kai hari

Falasdinawa na zaman dar-dar ganin yadda Isra’ila ke barazanar kai hari

Wani Bafalasdine dake zama a wani yanki dake Zirrin Gaza ya bayyana cewa ya na cikin hatsari sabili da isra’ilawa na barazanar iya kaiwa gidansa hari.

Ya bayyana cewa a yayinda kake zaune a gidanka na kogo da iyalinka wasu na iya kai maka farmaki. Barakat Mour mai shekaru 60 ya shaidawa kafar yada labaran Reuters akan irin barazanar da suke fuskanta a gidanjensu dake garin Hebron a yankin Zirrin Gaza.

Ya kara da cewa anan aka haifeni anan na tashi, wannan kogun gidana ne kuma ina daukarsa da muhinmanci.

Dakarun kasar Isra’ila dai sun bayyana cewa a cikin ‘yan kwanakin nan an samu tashin-tashina tsakanin Isra’ilawa da mazauna yankin koguna a kauyen At-Tuwani  dake yammacin Hebron lamarin da suka dauki mataki domin tabbatar da zaman lafiya.

Dangane ga kungiyar rights group ta B'Tselem na kasar Isra’ila, Falasdinawa dai sun kasance mazauna kogunan tun daga shekarar 1830 inda suke amfani da kokunan domin fakewa da kuma fake awakansu da tumakansu.


News Source:   ()