Falasdinawa 5 sun ji raunuka yayin shiga tsakani da sojojin Isra’ila suka yi a zanga-zangar adawa da kafa haramtattun matsugunan da Yahudawa ke yi a yankunan da ke karkashin mamaya.
Majiyoyin yankin sun bayyana cewa Falasdinawan sun gudanar da zanga-zangar mayar da martani ne kan kafa haramtattun matsugunan Yahudawa a karkarar garin Bayta da ke Nablus.
An bayyana cewa, sojojin na Isra'ila sun mayar da martani ga masu zanga-zangar da harsasan roba da hayaki mai sa hawaye.
A cikin wata sanarwa da Kungiyar ba da agaji ta Falasdinu ta fitar, an bayyana cewa sojojin na Isra'ila sun raunata mutane 5 da harsasai na roba, kuma hayakin mai sa hawaye ya shafi mutane da dama.