Falasdin ta gargadi Isra'ila game da mamayar yankunanta

Falasdin ta gargadi Isra'ila game da mamayar yankunanta

Ministan Harkokin Waje na Falasdin Riyadh Al-Maliki ya gargadi Isra'ila da cewar, za a samu sakamako mai tsauri game da mamayar yankunansu da take yi.

A jawabin da Al-Maliki ya yi a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga kasashen duniya da hukumomin kasa da kasa da su dauki matakai ingantattu don hana Isra'ila ci gaba da mamayar yankunan Falasdinawa.

Maliki ya ce mamayar ba ta bisa ka'ida, kuma hakan zai sake jefa alakar Isra'ila da Falasdin cikin mummunan yanayi, inda za a samu mummunan sakamakon wannan mataki.

Maliki ya yi kira ga dukkan kasashen duniya da su amince da Falasdin a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Ya ce "Kowacce kasa tana da karfin ikon sauya wannan wasa kafin lokaci ya kure, tana da karfin dakatar da Isra'ila da kuma samar da tsarin warware rikicin ta bangaren biyan bukatun kasashe 2."


News Source:   www.trt.net.tr