Fafaroma Francis na darikat Katolika ya gana da shugaban shi'a a kasar Iraki Ali Al-Sistani a yayinda ya kai ziyara a kasar.
Kamar yadda kanfanin dillacin labaran kasar Iraki ta sanar daga filin tashi da saukar jiragen saman Iraki an kai Fafaroma zuwa gidan Al-Sistani. Shugabanin biyu sun tattauna akan harkokin addini.
Fafaroma Farancis ya kuma tattauna da firaiministan Iraki Mustafa Al Kazimi da shugabana kasar Iraki Berhem Salih a babban birnin kasar Baghdah.
Daga bisani Fafaroman ya kai ziyara a husaimiyar Seyyidat Nejat.
Daga nan kuma ya garzaya zuwa garin tarihin Ur inda ya ziyarci gidan tarihin Nasiriye.