Ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Turkiyya Dkt Fahrettin Koca domin kara kange yaduwar Korona ya yi kira ga al’umman kasar da su nisanta kasansu daga cunkoson jama'a da kuma guraren dake rufe a cikin wannan lokaci na hunturu.
Minista Koca ya kara kira ga al‘umma da su cigaba da mutunta dokoki da kuma bin shawarwarin da ma’aikatan lafiya suka bayar akan yaki da kwayar cutar Korona.
Kawo yanzu dai kwayar cutar COVID-19 ta yi sanadiyar rayuka fiye da miliyan 1.49 a kasashe 191 a fadin duniya.