Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa da kasa watau CDC ta yi kira ga al’umma da su bi wasu ka’idojin da aka ta’alaka akan amfani da mask -takunkumin rufe fuska.
Hukumar CDC ta bayyana a shafinta ta Twitter da cewa ya zama wajibi a sanya mask musanman ga wanda zai fita waje ko zai je inda akwai dinbin mutane.
Ya kamata kuma a rinka yin numfashi daga cikin takunkumin sabili da haka ya kamata takunkumin ya rufe hanci da baki.
Idan takunkumin wanda ake iya wankewa ne ya zama wajibi a wanke shi duk lokacin da aka dawo gida.
Haka kuma hukumar ta yi kira da kar a sanyawa yara ‘yan kasa da shekaru biyu kuma kada mutum y iyi anfani da kayayyakin kariya na likitoci in har shi ba likita ko ma’aikacin lafiya bane