A yayinda likitoci ke bayyana cewa sanya takunkumin rufe fuska baida wata cutarwa ga bil adama suna kuma kira da a kula da yara yayin da suke sanye da ita domin zai iya haifar musu da matsalar yin numfashi.
Baya ga yara kuma duk wanda bai iya cire takunkumin da kansa ka iya fuskantar matsalar shakewar numfashi idan yana sanye da takunkumin.
Baya ga wannan kowa zai iya sanya takunkuman rufe fuska ba tare da ya fuskanci matsala ba sabanin shaci fadin da ake yadawa a cikin al’umma.
Masana kiwon lafiya kuma sun kara da cewa sanya takunkumin rufe fuska ka iya rage hadarin yaduwar kwayar cutar corona a cikin al’umma.