Facebook ta sanyawa shafukan sojojin da suka yi juyin mulki a Myanmar takunkumi

Facebook ta sanyawa shafukan sojojin da suka yi juyin mulki a Myanmar takunkumi

Kanfanin Facebook ya sanar da sanyawa shafukan sojojin da suka habbarar da gwamnatin farar hula a kasar Myanmar takunkumi.

A wata sanarwar da kanfanin Facebook ya sanar a rubuce, shafukan sojojin Myanmar na yada bayanai da basu da hujja sabili da haka an takaitasu.

Sanarwar ta kara da cewa duk da ya ke ba za a rufe shafukan baki daya ba amma za a dauki matakan takaita abubuwan da zasu rinka yadawa.

Daga cikin wadanda aka sanyawa shafukansu na Facebook takunkumi har da na Birgediya Janar Zaw Min Tun.

 


News Source:   ()