Faɗa tsakanin ƙungiyoyi ya hallaka mutane 100 a iyakar Syria da Turkiya

Faɗa tsakanin ƙungiyoyi ya hallaka mutane 100 a iyakar Syria da Turkiya

Tun cikin daren Juma’ar da ta gabata ƙazamin faɗan ya ɓarke a ƙauyukan da ke kewaye da birnin Manbij tsakanin ɓangarorin biyu har zuwa jiya Lahadi, inda ƙididdiga ta nuna cewar rayukan mayaƙa 101 ne suka salwanta, 85 a ɓangaren mayaƙan sa kai da Turkiya ke marawa baya, yayin da mayaƙan Kurdawa na SDF suka rasa dakaru 16.

Tun a ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata mayaƙan sa kai da Turkiya ke taimakawa suka ƙaddamar da farmakin neman murƙushe dakaru Kurdawa na SDF, a dai dai lokacin da ‘yan tawayen HTS suka ƙaddamar da hare-hare kan sojin Syria wanda ya basu damar ƙwace ƙasar cikin kwanaki 11 tare da kifar da gwamnatin Bashar al Assad.

A baya bayan nan ne kuma jagoran sabuwar gwamnatin Syrian, Ahmed al-Sharaa ya sanar da shirin shigar da mayaƙan Ƙurdawan na SDF cikin sabuwar rundunar sojin ƙasar.

Wasu bayanai sun ce ko a yammacin jiya Lahadi an samu fashe-fashe a ginin da ke zaman rumbun adana makaman rundunar sojin tsohuwar gwamnatin Bashar al-Assad da ‘yan tawaye suka kifar, hare-haren da ake kyautata zaton jiragen yaƙin Isra’ila ne suka kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)