Darakta Janar na Gifan Rediyo da Talabijin na Turkiyya (TRT) Ibrahim Eren ha bayyana cewar, taron TRT World Forum ya zama.mai jiyar da amon marasa amo.
Eren ya yi jawabi a wajen bude Taron TRT World Forum 2020 da ake gudanarwa ta yanar gizo sakamakon annobar Corona.
Taron na bana da za a yi a tsakanin 1 da 2 ga Disamba na da taken "Sauyar Duniya Bayan Annobar Corona" inda kwararru, shugabannin al'uma da malaman jami'o'i suke tattauna muhimman batutuwa.
Ya ce, tun bayan fara taron wanda wannan ne karo na 4, ya zama mai nunawa duniya cewar ana bukatar a rayu tare, duniya na bukatar juna don wanzuwa.
Darakta Janar na TRT ya ci gaba da cewa, sakamakon wannan ya sanya ake ta jiyar da amon wadanda ba sa iya jiyarwa, ana ta yin gwagwarmayar ganin wannan abu ya tabbata.
Ya ce, wannan ce falsafar da aka assasa TRT World a kai, kuma tana ci gaba da tafiya a kan ta.