Shugaba kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya halarci bikin bude Masallacin Uzun Mehmet da ke Zonguldak a kasar Turkiyya.
A jawabin da ya yi yayin bude masallacin, wanda aka gina a wani wuri da ke kallon teku, inda kusan mutane dubu 6 za su iya yin salla a lokaci guda, Erdogan ya ce "duk da cewa zamani ya canza, zurfin kiyayya ga Kasar Turkawa ba ta taba canzawa ba."
Da yake bayyana cewa "wadanda ba za su iya jure wa tutar Turkiyya ba, sun fara kai hari ga hadin kai da hadin kan al'umma, ba sa jinkirin kai hari masallatai,"
"Ba za su iya tarwatsa hadin kanmu ba. Duk da haka kungiyoyin 'yan ta'adda da yawa da makiya Turkiyya ke amfani da su, tun daga FETO (Kungiyar' Yan Ta'adda ta Fethullahist) zuwa PKK, sun fara kai hare-hare a Masallatanmu, addinin kasarmu, addininmu da imaninmu."
Erdogan ya kuma kara da cewa,
"Hakkinmu ne mu kunyata makiya masu kushe muna, aikinmune, hakkinmu ne mu kalubalanci masu adawa damu"