Erdogan ya yi kira ga kasashen duniya game da riga-kafin Corona

Erdogan ya yi kira ga kasashen duniya game da riga-kafin Corona

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga kasashen duniya da suke da isasshiyar allurar riga-kafin Corona ga 'yan kasashensu da su aika sauran zuwa ga kasashe mabukata.

Shugaba Erdogan ya aike da sakon bidiyo ga taron shugagannin kasashe da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya ta yanar gizo mai taken "Daukar Nauyin Cigaba Bayan Corona".

A sakon na Shugaba Erdogan ya ce, "A lokacin da ake da kasashen da suka yi wa kusan dukkan 'yan kasashensu allurar riga-kafin Corona, a gefe guda kuma akwai biliyoyin mutane da ko ta farko ba su samu an yi musu ba."

Ya ce, "Batun allurar riga-kafin Corona ya zama wani yanayi mummuna. Muna ganin yadda har yanzu kusan kasashen duniya 100 ba su samu allurar riga-kafin ba."

Erdogan ya ci gaba da cewa, "Asali idan ba a janye rashin adalci da daidaito wajen samun alluran ba, to ba za a magance cutar gaba daya ba, ba za a iya farfadowa daga matsalar tattalin arziki ba. Akwai bukatar kasashen da suka kammala yi wa 'yan kasarsu allurar, su aika sauran zuwa kasashen da suke bukata."

Shugaba Erdogan ya kara da cewa, idan aka kammala samar da alluran riga-kafi a Turkiyya, za su isar da su ga dukkan bil'adama ta hanya saukakka.


News Source:   ()