Erdogan ya yi kira da a kafa katabaren bankin Musulunci mai suna "Mega Bank " na kasa da kasa

Erdogan ya yi kira da a kafa katabaren bankin Musulunci mai suna "Mega Bank " na kasa da kasa

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga kasashen musulmi na D-8 da su kafa katabaren bankin Musulunci mai suna "Mega Bank"

Shugaba Erdogan ya halarci taron kolin kungiyar D-8 karo na 10 da aka gudanar ta yanar gizo. 

Erdogan dake bayyana cewa zai mika ikon jagorancin na shekara hudu ga hannun Bangladesh nan bada dadewa ba ya kara da cewa,

"Sakateriyar kungiyar da ta kasance a Istanbul tun daga kafata an gudanar da muhimman ayyuka wadanda kuma za a ci gaba da gudanarwa. 

A yayinda da Erdogan ke bayyana irin muhimmancin hadaka tsakanin kasashen musanman a halin yanzu da Korona je ci gaba da addabar duniya ya jaddada cewa,

Allurar rigakafin korona da aka samar a kasar Turkiyya zai kasance wanda ko wani bil adama zai iya amfana ba tare da wariya ba.

Shugaba Erdogan ya bayyana cewa kasar Turkiyya ta kaddamar da tsarukan da zasu sauwaka kasuwanci tsakaninta da mambobin D-8 kuma za a aika da takardan neman hakan ga kasashen da lamarin ya shafa. 

Erdogan ya kara da cewa kasashen musulmi na bukatar shirin tsarin samar da kudade wanda ya kamata a kafa katabaren bankin Musulunci mai suna "Mega Bank " da zai tabbatar da hakan. 

Erdogan, ya kara da cewa kasashenmu na fuskantar matsalar canjin kudi, wannan bankin ka iya magance wacannan matsalar. 

Ya kuma kira da a kasance tare da kasar Falasdin wacce ke gwagwarmayar yaki da zalunci da kuma fatara; da kuma taimakawa ýan gudun hijirar kasashen Yemen, Siriya da Arakan. 


News Source:   ()