Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Sanarwar da Sashen Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya ta fitar ta ce a tattaunawar shugabannin an tabo batun hadin kai don yaki da annobar Corona(Covid-19) da kuma alakar Turkiyya da Jamus.
A tattaunawar ta Shugaba Erdogan da Merkel an kuma tabo batutuwan rikicin Libiya da Siriya da ma yankunansu baki daya.