Erdogan: Babbar manufarmu ta yaki da ta'addanci ita ce kawar da barazana

Erdogan: Babbar manufarmu ta yaki da ta'addanci ita ce kawar da barazana

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, game da "Farmakan Kambori-Walkiya da Kambori-Walkiya" kan kungiyar ta'addar a ware ta PKK da ke arewacin Iraki, ya bayyana cewa, manufar ita ce samar da lumana.
Erdogan ya kara da cewa,
"Manufarmu ita ce kawar da kasancewar 'yan ta'addar kwata-kwata daga yankin da kuma kokarin samar da lumana a iyakokinmu na kudanci da kuma kawar da barazanar."

A yayinda shugaba Erdogan ke jawabi a Cibiyar Umurnin "Farmakan Kambori-Walkiya da Kambori-Walkiya", da aka kafa domin yakar kungiyar ta'adda a arewacin Iraki. Ya bayyana cewa,

"Manufarmu ita ce kawar da kungiyar ta'adda gaba daya da kuma kawar da barazanar daga iyakarmu ta kudanci. A kasashen Turkiyya, Iraki da Siriya 'yan ta'adda ba zasu taba samun wurin labewa ba. Ya kara da cewa zamu ci gaba da gwagwarmaya har sai mun kawar da wadannan gungun masu kisan gilla wadanda ba su kawo komai ba sar barna"

Erdogan dake bayyana cewa mun yi nasarar kauda mabuwa, ma'adana da makaman 'yan ta'adda da dama kuma ba zamu yi kasar a gwaiba ba har sai mun gaba bayan dan ta'adda na karshe a yankin. Kasanccewar amfani da makaman da aka kera a cikin gida wajen yaki da ta'addanci a yankunan abin farin ciki ne da muke alfahari dashi.


News Source:   ()