Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa kamar yadda muka ciki alkawuran da muka yi wa al'ummanmu a cikin shekaru18 haka kuma zamu cika alkawarin da muka yi na yaki da Covid-19 da haka wadanda ke ganin Turkiyya zata gaza zamu kunyatasu.
Erdoğan, ya yada a shafinsa ta Twitter da cewa,
"Wannan kalaman namu ba zancen baka bane kawai, zane ne akan dutse. Tamkar dai yadda muka cikawa al'ummanmu alkawuran da muka yi musu a cikin shekaru 18 haka kuma zamu ciki alkawarin yin nasara da yakar coronavirus. Wadanda ke ganin Turkiyya ba zata iya ba zamu sake basu haushi"