Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya tatauna da shugabanin Azerbaijan Iran , Oman, Turkmenistan , Aljeriya , Tunusiya, Kırgızistan da na Irak inda suka yiwa juna barka da salla.
Shugaba Erdoğan ya tatauna da shugabanin Azerbaijan Ilham Aliyev, na Iran Hasan Ruhani, Oman Sultanı Heysem bin Tarık, Turkmenistan Kurbankulu Berdimuhammedov, Aljeriya Abdülmecid Tebbun, Tunusiya Kays Said, Kırgızistan Sooronbay Ceenbekov, Irak Berhem Salih da mataimakin shugaban majalisar Bosnia and Herzegovina Bakir İzetbegoviç inda suka yiwa juna barka da salla.
Kamar yadda ma'aikatar sadarwar Turkiyya ta sanar shugabanin sun taya juna murnar babban sallah. Bayan haka shugabanin sun aminta akan bunkasa huldan dake tsakaninsu da kuma inganta lamurkan yankin baki daya.