Erdoğan ya taya Ibraniyawa murnar sabuwar shekarar Rosh Hashanah

Erdoğan ya taya Ibraniyawa murnar sabuwar shekarar Rosh Hashanah

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya fitar da sakon taya murna game da bikin Rosh Hashanah, wanda ya dace da 18-20 ga Satumba 2020 bisa kalandar Ibraniyanci.

Kamar yadda ma'aikatar sadarwar kasar Turkiyya ta sanar, da yake taya Yahudawa murna, shugaba Erdoğan ya jaddada cewa, zamantakewa, juriya, hakuri da soyayya sun kasance alamomin siyasa, al'adu, da kuma ire-irensu sun kasance dabi'u mafi alfano da suka hada kan al'umman wadannan kasashe.

Erdoğan, a sakonsa ya kara da cewa:

"A wadan nan ranaku na musamman da har da 'yan ƙasarmu masu addini daban ke rayuwa cikin aminci da 'yanci, suna kuma kara karfafa addinanmu da al'adunmu ta hadin kai; tare da waɗannan tunani, ina yi wa dukkan Yahudawa, musamman ma' yan ƙasarmu, a yayin bikin Rosh Hashanah murnar wannan mahimman hutu na addininsu "

 


News Source:   ()