Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya mayarwa takwaransa na Faransa Emmanuel Macron da martani.
Erdoğan a taron karawa juna sani da aka gudanar na Tsibirin Demokradiyya da 'Yancin ya bayyana cewa,
"Ya shugaba Macron, zamu iya kara samun matsala tsakaninmu da kai sosai. Kai baka san tarihi ba , baka ma san tarihin Faransa ba, da farko, ka yi fama da al'umma Turkawa, kar kayi katsa landan a Turkiyya."
A jawabin shugaba Erdoğan, a yayinda TASHIN HANKALI KE KARUWA A GABASHIN BAHAR RUM ya yi kira ga kasar Girka.
"Girka idan aka zo batun iyakan kasa kina cewa mu makota, makota, makontan ki ne. Sabili da haka ya zama wajibi ki bayar da hakkin makotaka. Kar ki bi gurbataciyar hanya, wannan hanyar da kika kama ba zai haifa miki da mai ido ba, za ki kasance ke tilo"
Shugaba Recep Tayyip Erdoğan dake bayyana cewa Turkiyya ta ishi kanta ya kara da cewa,
"A halin yanzu bamu da kofa a Asusun Lamunin IMF, mun ishi kanmu, wacannan kasar ta wadatar da kanta"