Erdoğan ya kyamaci farmakin da 'yan sanda suka kai wa Masallacin Maulana a Jamus

Erdoğan ya kyamaci farmakin da 'yan sanda suka kai wa Masallacin Maulana a Jamus

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, ya kyamaci farmakin da 'yan sandan kasar Jamus suka kaiwa Masallacin Maulana dake Berlin babban birnin Jamus.

Shugaba Erdoğan ya yada a shafinsa ta twitter da cewa,

"Muna masu matukar kyamar matakin 'yan sandan Jamus a Masallcin Maulana a Berlin dake nuna kyama da wariya ga Musulmi da addini Islama"

A yayinda da Erdoğan ke yiwa shugabanin da mabiyan Masallacin jaje, ya kara da cewa a Turkiyya bamu taba nuna wariya ko kyama ga ko wace irin addini ba.

Shugaba Erdoğan ya ci gaba da cewa zamu ci gaba da daukar matakan kalubalantar kyamatar baki da nuna musu wariya a doron kasa.

Ya kara da cewa abin bakin ciki ne yadda Turai dake ikirarin demokradiyya shekara da shekaru, a yanzu ta juya baya tana aikata laifukan da suka take 'yancin demokradiyya.

 


News Source:   ()