Erdoğan ya gargadi Tarayyar Turai akan shagwaba Girka

Erdoğan ya gargadi Tarayyar Turai akan shagwaba Girka

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewar ya kamata Tarayyar Turai ta fahinci cewa shagwaba Girka da take yi tana sabawa tare da kaucewa ka'idoji da dabi'o'inta ne.

Shugaba Erdogan da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatin Dolmabahçe dake Istanbul ya bayyana labari mai dadi na cewa Turkiyya ta gano rumbun iskar gas da ya kai yawan cubic meter biliyan 320 a cikin tekun Bahar Aswad.

A yayinda yake nuni da cewa makamashi na da matukar muhimmanci a lamurkan bunkasa da kare ‘yancin kasa, Erdogan ya bayyana cewa suna fatan samun irin wannan labari mai kyau a gabashin tekun Bahar Rum.

Erdoğan dake nuni da cewa wadanda ke neman tada zaune tsaye a tekun Bahar Rum basu kasance don komai ba face domin mallakar iskar gas, ya kuma kara da cewa,

“A kasarmu mun dogara akan warware matsalar makamashi daga tushe. Akan lamarin makamashi ba zamu yi kasa a gwiwa ba; ba kuma zamu huta ba. Ba zamu ci hakkin kowa ba; ba kuma zamu yarda da wani ya ci hakkinmu ba."

Da yake tsokaci akan ayyukan da Girka ke yi ita tilo na hydrocarbon a cikin tekun Bahar Rum, Erdogan ya kara da cewa ya kamata Tarayyar Turai ta sani da cewa shagwaba da goyon bayan rashin hujja da take baiwa Girka akan hakan ta na sake bayyana sabawa ka'idojinta da dabi'unta ne.

 


News Source:   ()