Dutsen Taal mai aman wuta ya motsa sau 185

Dutsen Taal mai aman wuta ya motsa sau 185

Dutsen Taal mai aman wuta da ke kudancin Manila Babban Birnin Filifins ya yi aman wuta sau 185.

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun rawaito Hukumar Nazari Kan Duwatsu Masu Aman Wuta da Girgizar Kasa na cewa, a awanni 24 da suka gabata Dutsen Taal ya yi girgiza sau 185 wanda hakan ya sanya aka daga matakin gargadi zuwa mataki na 3.

A ranar 1 ga watan Yuli ne aka lura da dutsen ya fara aman wuta inda nan da nan aka fara kwashe jama'ar da ke kewayensa.

 


News Source:   ()