An bayyana cewa Dutsen Taal Volcano, wanda ke kudu da Manila, babban birnin Philippines, ya kai mataki na 3 a yayinda yake kusa da fashewa.
A cewar kafar labaran Bloomberg, a cikin bayanin da Cibiyar Nazarin Kimiyyar Kasa ta Philippines ta yi, an bayyana cewa Dutsen Taal Volcano ya kai mataki na 3 bayan da ta fitar da tururi da barbashi.
Mahukunta sun ba da shawarar a kwashe mutanen dake kauyukan da ke kusa da dutsen mai fitad da wuta saboda yiwuwar aman wuta da hatsarin tsunami.