An samu karar fashewa da aman wuta tare da bakin hayaki a Dutsen Otake da ke Tsaunin Suwanose na jihar Kagoshima ta Japan.
Hukumar Kula da Yanayi ta Japan ta bayyana cewa, da misalin karfe 02.57 ne fashewar ta afku, kuma wutar da dutsen ya yi amai da karfi ta kai nisan kilomita 1.
Kamfanin dillancin labarai na Kyodo ya sanar da cewa, mahukuntan ba su bayyana mutuwa ko jikkatar wani a yankin da dutsen ya ke ba.
An gargadi jama'a da kar su kusanci dutsen mai aman wuta, kuma ibtila'in na a mataki na 3.
Haka zalika an yi gargadin cewa, akwai yiwuwar dutsen ya sake aman wuta wadda za ta iya kai nisan kilomita 2.
Dutsen Otake mai aman wuta a Tsibirin Suwanose, na da nisan kilomita 230 kudu da jihar Kagoshima ta Japan.