An sanar da cewa dutsen Merapi Volcano dake tsibirin Java a kasar Indonisiya ya fashe bayan ya kwashe kwanaki ya na fitar da wuta.
A cikin bayanin da Cibiyar Fasaha da Bincike akan Bala'i ta Kasa (BPPTKG) ta yi, an bayyana cewa toka da hayaki sun tashi daga dutsen da ya fashe har na tsayin mita dubu.
Jami'an BPPTKG sun yi gargadin cewa kada a yi wani aiki har zuwa kilomita 5 a kusa da dutsen mai fitad da wuta, lamarin da ya karu a kwanakin nan.
Fashewa ta karshe da Merapi Volcano ta yi ta afku ne a ranar 9 ga watan Yuni.