Dutsen dake kan tsibirin Java dake kasar Indonesia mai aman wuta ya fashe har sau biyu.
Kamar Yadda Hukumar Kula da Yanayin kasar ta (BPPTKG) sanar dutsen Merapi mai aman wuta wanda ke garin Yogyakarta ya fashe har sau biyu tsakanin karfe 08.02 da 12.50.
Toka da burbudin da ya fita daga dutsen sanadiyar fashewarsa sun yi tafiyar fiye da mita 200.
An dai yi kira da al'umma da su nisanta kansu da kusan kilomita biyar daga dutsen.
Kasancewar ganin al'umman yankin Megaland cikin hadari ya sanya kwashesu zuwa wani wuri mai sukuni.