An sanar da cewa dutsen Etna mai aman wuta dake tsibirin Sicilya dake kasar Italiya ya sake fashewa.
Dutsen da ya kasance mafi tsayi da kuma yin aman wuta a Nahiyar Turai ya yi wani fashewa mai ban tsoro da ya fitar da burbushi masu yawan gaske.
Duthen da tsayinsa ya kai mita dubu 3 da dari 330 tokarsa ya mamaye dukkanin yankin da yake.
An dai tabbatar da cewa dutsen Etna mai aman wuta ya fashe sau da yawa a cikin shekara.
A watan jiya ma ya yi wani irin fashewa.
An dai bayyana cewa a shekarar 2002 ne ya yi wani irin fashewar da bai taba irinsa ba.