Dutsen Etna da ke Italiya ya yi bindiga da fara aman ruwan wuta

Dutsen Etna da ke Italiya ya yi bindiga da fara aman ruwan wuta

An samu fashewa mai karfi tare da aman ruwan wuta a dutsen Etna wanda na daya daga cikin duwatsu masu aman wuta a kudancin Italiya.

Bayan karar da dutsen ya fitar a ranar Talatar nan ne sai aka fara ganin ruwan narkakkiyar wuta na zuba daga cikin sa.

Sakamakon fashewar dutsen an samu bakin hayaki da ya mamaye sararin samaniyar garin Catania. Hayakin ya mamaye wurare da dama.

Sakamakon bakin hayakin da ya mamaye sama saboda bindigar da Etna ya yi, an samu tsaiko a safarar jiragen sama a yankin. An dakatar da dukkan tashi da saukar jiragen sama tare da aiyana dokar ta baci a filin tashi da saukar jiragen sama na Fontanarossa da ke Catania.

Hayakin da ya fita ya yi nisan kilomita 1 a sama wanda hakan ke barazana ga tsaron jiragen sama.

A watan Janairu ne dutsen Etna da ke Sicilia ya yi aman wuta na karshe.


News Source:   ()