Wani jariri ya mutu a cikin wani filin wasa da dusar kankara a Norilsk dake Siberia.
Sabili da yawan dusar kankaran gidaje hudu sun nutse a cikinsa.
Sakamakon aikin ceton da aka fara a wani yanki na murabba'in mita 300, an tono gawar wani jariri daga cikin dusar kankara.
An kuma tono mutum hudu da suka hada da yara biyu a raye daga cikin dusar kankaran. Biyu daga cikinsu sun samu munanan raunuka.
Hukumar bayara da agajin Rasha ta bayyana cewa akwai wasu mutum 4-5 karkashin dusar kankarar.
Tawagar kusan mutane 200 na ci gaba da bincike a cikin yanayin sanyi wanda ya kai digiri 30 ƙasa da sifili.
Mahukuntan tarayyar Rasha sun fara bincike kan ko akwai sakaci a cikin lamarin mara dadi.