A Brazil, yanayin sanyi ya kai matakin da ba a taba ganin irin sa ba kuma ya afku ne sakamakon dusar kankara.
A Brazil, kamfanin binciken yanayi na Somar Meteorologia ya sanar da cewa sama da birane 40 a jihar Rio Grand do Sul sun sami kankara kuma aƙalla kananan hukumomi 33 sun sami dusar ƙanƙara.
Dusar kankara wadda ta fara a ranar 28 ga watan Yuli a kudancin kasar ta ci gaba. Hakanan ana tsammanin yanayin sanyi zai ragu a jihohin Parana da Santa Catarina.
A halin da ake ciki, matsanancin sanyi ya shafi samar da gahwa mai yawa, rarar sukari da shukar lemu.
Yanayin sanyi a Brazil, wanda shi ne kan gaba wajen samar da gahwa a duniya, ya kuma ƙara farashin gahwa da sukari na kasa da kasa.