Duniya tana da shekaru biliyan 1 na iskar oxygen

Duniya tana da shekaru biliyan 1 na iskar oxygen

Hukumar Bincike kan Sararin Samaniya ta Amurka (NASA) ta yi hasashen cewa iskar oxygen, tushen rayuwar duniya za ta kare a cikin shekaru biliyan 1 masu zuwa saboda karuwar hasken rana wanda zai iya yin lahani ga bil adama.

A cikin binciken da NASA ta gudanar, an tsara yanayin duniya, tsarin halitta da tsarin kasa.

Dangane da haka, hasken rana zai ƙaru da lokaci kuma zai kara zafin yanayi, ɗumamar yanayin zai haifar da sauyi ga iskar carbon dioxide kuma hakan zai lalata tsirrai ya saka su mutu.

Tare da mutuwar shuke-shuke da ke samar da iskar oxygen, iskar oxygen a duniya za ta kare kuma duniya za ta zama wurin da ba za a iya rayuwa a ciki ba.

An yi nuni da cewa wannan halin yana afkuwa a hankali sosai, don haka baya shafar rayuwar yau da kullum na yanzu.

An yi iƙirarin cewa shekaru biliyan 1 daga yanzu, adadin iskar oxygen zai kasance a matakin da dukkan abubuwa masu rai ba za su iya rayuwa a duniya ba.


News Source:   ()