Duniya ka iya fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru 80 da suka gabata

Duniya ka iya fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru 80 da suka gabata

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Guterres ya yi gargadin cewa duniya na iya fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru 80 da suka gabata.

Dangane ga Sputnik, Guterres da ke halartar bikin ba da lambar yabo ta Nobel ta Duniya ta yanar gizo ya bayyana cewa,

“Sabuwar nau'in kwayar cutar Korona ta na cigaba da tabarbare lamurkan walwala, jin dadin al'umma da tattalin arziki. Nakasun da Covid-19 ta haifar babu wata allurar raiga-kafin da zata iya gyara shi. Muna fuskantar koma bayan tattalin arziki mafi girma a cikin shekaru tamanin da suka gabata.”

Da yake bayyana cewa tsananin talauci yana karuwa a duk fadin duniya kuma barazanar yunwa na kara gabatowa, Guterres ya lura cewa kasashe ba za su iya hada kai don magance matsalar kwayar cutar Korona ba.

Ya kara da cewa wacannan annoba ce dake kalubalantar duniya baki daya, wacce babu kamarta. Sai dai abin bakin ciki ne yadda gwamnatoci suka kasa daukar matakin bai daya akanta.

 


News Source:   ()