Cikin wani sabon rahoto da UNICEF ya fitar ya nuna yadda binciken asusun na baya-bayan nan ke bankaɗo ƙaruwar cin zarafin yara a lokacin ƙuruciya.
A cewar UNICEF idan aka yi jumulla da adadin yaran da ke fuskantar cin zarafi ko kalaman batsa a lokacin ƙuriciya wadda a wasu lokutan kan kai ga fyaɗe alƙaluman na matsayin duk yarinya 1 a cikin cikin 5 ko kuma adadin yara mata miliyan 650 iyakar wanda ake samun rahotannin faruwarsu.
Cikin shekara guda, hukumar HISBA a jihar Sokoto ta samu laifukan fyade fiye da 600. Daily TrsutRahoton na UNICEF wanda asusun ya yi laƙabi da ‘‘buɗe sabon babi’’ duk da cewa yara mata suka fi fuskantar cin zarafin amma akwai tarin maza da suma kan fuskancin cin zarafin ta hanyar fyaɗe.
A cewar rahoton bincikenta ya nuna cewa duk yaro 1 cikin 11 ko kuma yara maza miliyan 240 zuwa 310 sun fuskanci cin zarafi ta hanyar fyaɗe gabanin kaiwa shekaru 18 da haihuwa.
Matsalar yi wa mata fyade ta ta'azzara a Najeriya. Daily TrustUNICEF ya ce abin takaici ne yadda matsalar ke ci gaba da ta’azzara duk da cewa da dama kan ɓoye bayanan faruwar makamantan cin zarafin saboda fargabar nuna musu ƙyama ko kyara ko kuma tsana a cikin jama’arsu.
Wannan rahoto na UNICEF na zuwa a dai dai lokacin da ake gab da gudanar da babban taron ƙasa da ƙasa kan yaƙi da cin zarafin ƙananan yara da zai gudana a Colombia cikin watan gobe.
Asusun na UNICEF ya bayyana buƙatar da ke akwai ta ɗaukar matakan gyara don baiwa yara kariya musamman a lokacin ƙuruciya.
A cewar UNICEF ƙasashen kudu da saharar Afrika su ke kan gaba wajen fuskantar wannan matsala da aƙalla kashi 22 dai dai da yara mata miliyan 79 sai kuma gabashi da kudu maso gabashin Asiya da yara miliyan 75 kana wasu miliyan 73 a tsakiyar Asiya sannan miliyan 68 a Turai da arewacin Amurka kana miliyan 45 a kasashen Latin Amurka sannan wasu miliyan 29 a arewacin Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI