A kasar Turkiyya an sanar da kame mambobin kungiyar ta’addar Deash wadanda ake kuma kira ISIS har su 340 a cikin watan Disamban shekarar 2020.
Kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar a cikin watan Disamba jami’an tsaron kasar Turkiyya sun kame akallan ‘yan ta’dda 47.
Kotu dai ta tasa kyeyar wasu 34 daga cikinsu zuwa gidan wakafi inda kuma aka kori sauran zuwa kasashensu a yayinda ake kuma cigaba da sauraren karar wasunsu.
A wasu farmakai da aka kai a Ankara babban birnin kasar Turkiyya ‘yan sanda sun kame wasu ‘yan kasar Iraki su 18 wadanda ake zargin mambobin kungiyar ta’addar Deash ne.