An sanar da nasarar magance wasu 'yan ta'addan PKK 4 a yayinda suke shirin kai harin ta'addanci a yankin Metina dake Arewacin Iraki.
Ma'aikatar harkokin tsaron kasar Turkiyya ta yda a shafinta ta twitter da cewa an sake yin nasarar dakile shirin kungiyar ta'addar PKK.
A bincikin da ake yi ne aka gano wasu 'yan ta'addan PKK na shirin kai harin ta'addanci inda aka kai musu hari ta sama an ka kuma yi nasarar magance hudu daga cikinsu.