Dakarun kasar Turkiyya sun magance wani dan ta'addan PKK da ake nema ruwa jallo a yankin Hatay Amanos dake kasar.
Rundunar sojan kasar Turkiyya ce ta sanar da cewa daga cikin 'yan ta'adda hudu da aka magance a yankin tsaunin Amanos dake karkashin guindumar Hatay daga daga cikinsu mai suna Ibrahim Sengul ya kasance wanda ake nema ruwa jallo.
Ministan harkokin cikin gidan Turkiyya Suleyman Soylu ya yada wannan labarin a kafar sadar da zumuntansa ta twitter, inda yake cewa,
"Daga cikin 'yan ta'adda hudu da jaruman kasarmu suka magance akwai kusungumi daya da ake nema ruwa jallo. Ina mai taya jarumanmu murnar magancew dan ta'addan da ake yiwa lakabi da Bedrettin-Bedirhan wanda ainihin sunansa Ibrahim Sengul ne"