An sanar da taso kyeyar kusungumin dan ta'adda daga Iraki zuwa Turkiyya, dan ta'addan ya yi sanadiyar rasa rayukan sojoji 15 a wani harin bam da yakai a garin Kayseri.
An dai sanar da kame dan ta'addan ne da ya yi sanadiyar tayar da bam a motar sojoji a shekarar 2016 a garin Kayseri.
Ana yiwa dan ta'addan lakabi da Tekiner wanda ya kasance daya daga cikin masu haincin da aka sani da "Firat/Botan" an yi nasarar kama shi ne a aiki tukuru da jami'an leken asirin kasar Turkiyya da ta Jami'an tsaro suka gudanar.
A shekarar 2016 ne Ferhat Tekiner ya kai harin bam a motar sojoji lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayukan sojoji 15 da raunana 54.