Kakakin hukumar Mahmoud Basal ya ce Falasdinawan da suka rasa matsugunansu na zaman tsammani a kusa da hanyar Netzarim don komawa arewacin zirin Gaza, inda Isra'ila ta ki amincewa da su shiga yankunan su, yayin da ake takaddama kan musayar fursunoni tsakanin gwamnatin Yahudu da kuma Hamas.
Haka zalika, Hamas ta zargi Isra'ila da karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar hana Falasdinawa komawa arewacin Gaza.
Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da shawarar da shugaban Amurka, Donald Trump na mayar da Falasdinawan Gaza zuwa kasashen Masar da Jordan, tare da cewa hakan karfafa gwiwa ne ga masu aikata laifukan yaki.
Tuni ‘yan siyasar Isra'ila suka yi maraba da ra'ayin Trump na abin da ya kira tsabtace Gaza ta hanyar sauyawa mutane miliyan daya da rabi matsuguni zuwa kasashen Masar da Jordan.
A ranar Asabar ne, Donald Trump, ya umarci rundunar sojin Amurka, da ta mika wa Isra'ila wani nau'in bom mai cin matsakaicin zango, wanda magabacinsa Joe Biden ya hana gwamnatin ta Yahudu, bisa fargabar illar da zai haifar ga fararen hula a Gaza.
Shugaban na Amurka, ya kuma bukaci kasashen Masar da Jordan da su bawa Falasdinawan Gaza zama a kasashensu ko dai na wucin gadi ko kuma dindindin, yana mai cewa ya kamata a tsaftace Zirin Gaza baki dayansa.
Wannan kira na shugaban Amurka, ya jefa al'ummar Falasdinu cikin firginci, yayin da suke kallon sa a matsayin yunkurin fitar da su daga garuruwansu ta karfin tuwo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI