Dubun dan ta'adda Ercan Bayat ta cika a Turkiyya

Dubun dan ta'adda Ercan Bayat ta cika a Turkiyya

An sanar da kama  Ercan Bayat wanda ke da alhakin kai harin ta'addanci a garin Reyhanli da ke gundumar Hatay da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 53 a shekarar 2013.

An kama Ercan Bayat wanda aka bayyana a matsayin kusurgumin dan ta'adda a yankin Hatay tsakanin iyakar Turkiyya da Siriya. An dai mika shi ga jami'an tsaron yankin nan take.

A harin ta'addancin da aka kai a ranar 11 ga watan Mayu 2013 a garin Reyhanlı na tagwayen bama-bamai mutane 53 sun rasa rayukansu inda da yawa kuma suka jikkata.

 


News Source:   ()