Dubban mutane na tsarewa daga Florida na Amurka saboda guguwar Milton

Dubban mutane na tsarewa daga Florida na Amurka saboda guguwar Milton

Tun a ranar Talata shugaban Joe Biden ya gargadi milyoyin mutane da su gaggauta ficewa daga jihar, bayan da masana suka tattabar da cewa guguwar ita ce mafi ƙarfi da ake hasashen za ta haifar da mummunar ɓarna da ba a taba ganin makamanciyarta ba a cikin shekaru ɗari.

Duk da cewa akwai mutane kusan milyan 20 da ake rayuwa a yankunan da wannan guguwar za ta afka wa, amma mahukunta sun ce ya zama wajibi sama da milyan ɗaya su bar gidajensu saboda guguwar mai ƙarfin maki 5.

Kawo yanzu dubban mutane sun rasa wutar lantarki, yayin da aka rufe gidajen mai masu tarin yawa, kazalika kamfanoni da masana’antu ala dole suka bukaci ma’aikata su zauna gida har zuwa bayan saukar guguwar.

An hasashen cewa guguwar Milton za ta haddasa asarar dukiya ta aƙalla dala bilyan 60, sannan za ta kuɗin inshora ya ƙaru daga farkon shekara mai zuwa.

Biden na taimawa ƴan cin rani - Trump

Yayin shugaba Joe Biden ya sanar da jinkirta kai ziyara a ƙasashen Jamus da Angola saboda wannan guguwar, tare da alƙawarin bayar da duk taimakon da ya dace, a nasa ɓangare ɗan takarar adawa a zabe mai zuwa Donald Trump, ya ce a maimakon taimaka wa waɗannan Milton ta shafa, Joe Biden na amfani da dukiyaf Amurka ne domin taimaka wa ƴan ci-rani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)