Riƙe da tutocin Hizbullah da kuma hotunan Nasrallah, dubban magoya bayan ƙungiyar daga Lebanon da sauran ƙasashen yankin ne suka cika filin wasa na Camille Chamoun mai kujeru 55,000 da ke yankin kudancin Beirut.
Wata majiyar tsaro ta ƙasar Labanon ta kiyasta yawan mutanen da suka taru ya kai kimanin miliyan guda.
Kisan Nasrallah wanda ya jagoranci ƙungiyar ta mabiya Shi'a, ya biyo bayan tsawon shekaru da dama da aka kwashe ana gwabza fada tsakaninta da Isra'ila.
Sai dai shugaban kungiyar na yanzu, Naim Qassem, wanda aka watsa jawabinsa ga mahalarta taron ta wani babban majigi, ya ce Hizbullah, har yanzu tana nan da ƙarfinta, yayin da ake ganin kisan Nasrallah ya haifar mata da giɓi mai girman gaske.
Duk da cewa sojojin na Isra'ila sun janye daga kudancin Lebanon ɗin, amma har yanzu dakarun saman kasar na ci gaba da kai farmaki kan wuraren da suka ce yana karkashin ikon Hezbollah, kuma har yanzu sojojin na riƙe da ikon wasu yankuna biyar da ke kan iyakar ƙasar.
Sojojin Isra'ila sun kuma tsare fararen hular Lebanon da mayakan Hizbullah a kudancin ƙasar, yayin da suka tsare gawarwakin mayaƙan ƙungiyar da suka kashe.
Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a kudanci da gabashin ƙasar ta Lebanon a ranar Lahadin, inda suka yi ta shawagi a birnin Beirut a lokacin jana'izar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI