Donald Trump ya zama shugaban Amurka na 47 bayan sake nasarar lashe zaɓe

Donald Trump ya zama shugaban Amurka na 47 bayan sake nasarar lashe zaɓe

A jawabin da ya gabatar jim kaɗan bayan da ya samu nasarar lashe wakilan zaɓen 267 a wani yanayi da Kamala Harris ke da 214, kai tsaye Donald Trump ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara.

Bisa ƙa'ida ana son kowanne ɗan takara ya samu aƙalla Electoral Vote 270 gabanin iya jagorantar ƙasar.

Alƙaluman hukumar zaɓe sun nuna yadda Trump ya lashe kaso mai yawa na hatta manyan jihohin da ya gaza lashewa a 2016 da 2020.

Sa’o’i ƙalilan bayan fara ƙirgen ƙuri’un zaɓen Amurkan ne masana suka fara hasashen tsohon shugaban ya iya sake komawa kan kujerar shugabancin ƙasar.

Fatan samun nasara ya fara dusashewa ƴan Democrats ne bayan da Trump ya lashe 3 cikin jihohin ƙasar 7 da ake son kowanne ɗan takara ya lashe da suka ƙunshi Arewacin Carolina da Georgia da kuma Pennsylvania.

Tuni dai magoya bayan jam’iyyar Republican suka fara gangamin murnar nasarar lashe zaɓen.

Wannan nasara kai tsaye ta mayar da Trump shugaba na biyu da ya jagoranci Amurka sau biyu a mabanbantan lokaci tun bayan Grover Cleveland a 1892.

A shekarar 2016 ne Trump ya lashe zaben Amurka karon farko bayan doke Hillary Clinton amma kuma ya sha kaye a hannun Joe Biden yayin zaɓen ƙasar na shekarar 2020, shan kayen da ake alaƙantawa da annobar Covid-19 da ta ɓullo a wancan lokaci da kuma gazawar shugaban wajen magance cin zarafin da baƙar fata ke fuskanta wanda ya kai ga zanga-zangar Black Lives Matter.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)