Bayanai na nuna cewa tun bayan nasarar da Trump ya samu babu wani taro ko kuma ganawa da yayi ba tare da Elon Musk na wajen ba.
Bayan nada shi a matsayin shugaban sabuwar hukumar bibiyar ayyukan gwamnati da bangarorinta, Musk na dada samun shiga a sabuwar gwamnatin, ta yadda yakan halarci dukannin taro ko kuma ganawa da Trump ke yi tun bayan cin zabe.
An hango yadda ya yi 'uwa da makarbiya a yayin tafiya da kuma ganawar da Trump din yayi da Biden a baya-bayan nan.
To sai dai tuni ‘yan adawa ke ganin cewa wannan ya tabbatar da zargin da ake yi cewa Musk yayi amfani da kudi da kuma karfin kasuwanci wajen kwatarwa Trump mulki, don haka dole ya bashi damar fantamawa a gwamnatin.
Masu sharhi kan siyasa dai na ganin cewa wannan ka iya zama babban hadari ga kasar da kuma yadda take tafiyar da tsarin mulki, ganin cewa tun yanzu Trump ya fara baiwa Musk karfin da ya wuce kima, abinda ke kama da mulkin shugabanni biyu a kasa da daya.
To amma a daya bangaren wasu na ganin cewa wannan ba wani abun tayar da hankali bane, kasancewar mutanen biyu na da banbancin ra’ayi game da manufofin gwamnati, ta yadda watakila Elon Musk ya so yin amfani da ita don habbaka kasuwancinsa, da kuma jawo mutane a jika ko cikin Amurka, abinda Trump ke yaki da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI