Mataimakin daraktan ofishin shugaban kasar Stephen Miller ne ya tabbatar da ganawar da mutanen biyu suka yi a gidan talabijin na Fox News, inda ya bayyana cewa shugaban fasahar ya nuna karara cewa yana so ya goyi tsarin Trump na sabunta kasar Amurka karkashin jagorancinsa.
Mark Zuckerberg Shugaban Meta, iyayen kamfanin Facebook musamman, "ya bayyana goyon bayan sa da kuma nuna sha'awarsa na tallafawa da kuma shiga cikin wannan canjin da muke gani a duk faɗin Amurka.
Wasu daga cikin manhajojin Meta AP - Richard DrewMark Zuckerberg ya yi godiya ga gayyatar da aka yi masa a gidan Shugaba Trump don cin abincin dare da kuma damar ganawa da mambobin tawagarsa game da gwamnati mai zuwa," in ji mai magana da yawun kamfanin na Meta. Yayin da suka yi taka tsantsan a lokacin wa'adin farko na Donald Trump, shugabannin fasaha, kamar Elon Musk, sun yi gaggawar maraba da nasarar da ya samu a watan Nuwamba, kuma Mark Zuckerberg na daya daga cikin wadanda suka taya shi murna.
Donald Trump © Alex Brandon / APMark Zuckerberg ya ƙare ayyukan agajin da ya shafi zaɓe kuma ƙungiyarsa ta Meta ta kawo gyara tare da canza da dama daga cikin tsare tsare da nufin rage abubuwan siyasa a shafin Meta.
Shafin sada zumunta na Facebook yana daya daga cikin hanyoyin sadarwar zamantakewa da suka haramtawa Donald Trump wallafa ko kuma shiga cikin dandalin bayan harin da aka kai kan Capitol a ranar 6 ga Janairu, 2021.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI