Dole a matsawa Isra'ila shiga yarjejeniyar tsagaita wuta karo na 2 - Hamas

Dole a matsawa Isra'ila shiga yarjejeniyar tsagaita wuta karo na 2 - Hamas

An dai ci gaba da tattaunawa da nufin kai wa ga cimma jituwa don shiga rukuni na biyu na yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hamas a zaman da ake ci gaba da yi can a birnin alqahira na Masar, sai dai wasu bayanai sun ce duk da yadda ƙungiyar ke cewa a shirye take ta saki ilahirin fursunonin da ke hannunta don ƙulla yarjejeniyar dindindin, Isra’ila a nata ɓangaren taƙi amince da wannan tayin, inda maimakon shiga rukuni na biyu kai tsaye ta ke son tsawaita wa’adin rukuni na farko na yarjejeniyar zuwa aƙalla makwanni 6 a nan gaba, wanda zai baiwa dakarunta damar ci gaba da zama a sassan yankin na Falasɗinu.

Firaministan Isra’ila Banjemin Netanyahu ya bayyana cewa ƙasar shi na da fatan ci gaba da girke dakaru a Gaza na tsawon gomman shekaru, kuma yana da yaƙinin zai samu goyon bayan Amurka kan hakan, kalaman da ke zuwa duk da ƙoƙarin da ƙasashe ke yi na ganin ƙasar ta Yahudu ta janye daga ƙarfa-ƙarfar da ta ke yiwa Falasɗinawa a kusan dukkanin yankunansu.

Falasɗinawa dai na cike da fatan ganin an cimma yarjejeniyar musamman lura da yadda rukunin farko ke shirin kawo ƙarshe a gobe Asabar a wani yanayi da al’ummar yankin ke shirin tashi da azumin watan Ramadana dai dai lokacin da suke ci gaba da yashe ɓaraguzen gine-gine musamman a arewacin da Isra’ilan ta rushe kusan dukkanin gine-ginen yankin.

Bugu da ƙari wannan yanayi na zuwa a dai dai lokacin da Falasɗinawa ke kiraye-kirayen ganin Isra’ila ta basu damar damar gudanar da ibadunsu masallacin baitil maqadis bayan da ta girke dakaru a wajen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)